Hamas: Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Tana Goyon Bayan Palasdinu
Jami'i mai kula da alakar waje na kungiyar ta Hamas, Usama Hamdan ya ce Sun Ziyarci Iran ne domin samun goyon bayan kasashen musulmi ne akan sulhun palasdinawa.
A hirar da tashar telbijin din al-jazeera ta kasar Qatar ta yi da shi, Usama Hamadan ya kara da cewa; Taimakwa Palasdinawa da Iran take yi, wani abu ne da yake tabbatacce.
Jami'in na Kungiyar Hamas din ya kara da cewa; Hamas tana son samun goyon bayan kasashen larabawa da na yankin gabas ta tsakiya, akan sulhun da palasdinawa suka yi da junansu.
Har ila yau Usaman Hamadan ya kara da cewa Shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas, Isma'ila Haniyyah ne ya bude tattaunawa da kasashen larabawa da na yankin akan batun sulhu, wanda kuma kawo ya zuwa yanzu an sami sakamako mai kyau.
A ranar juma'ar da ta gabata ne dai kungiyar ta Hamas, bisa jagorancin Salih al-Aruri suka kawo ziyara nan Iran inda suka gana da jami'an gwamnati.