Larijani: Saudiyya Da "Isra'ila" Sun Hada Kai Wajen Fada Da Iran
Shugaban majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran Dakta Ali Larijani ya bayyana cewar Saudiyya tana ci gaba da hada baki da haramtacciyar kasar Isra'ila wajen fada da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Tashar talabijin din Press TV da ke watsa shirye-shiryenta daga nan Tehran ta bayyana cewar Dakta Larijanin ya bayyana hakan ne lokacin wani jawabi da ya yi a birnin Qum a jiya Alhamis inda ya ce akwai alaka da kuma aiki tare tsakanin "Isra'ila" da kasar Saudiyya a ci gaba da kiyayyar da suke nuna wa Iran da kuma ci gaba da dagula lamarin tsaron yankin Gabas ta tsakiya.
Dakta Larijani ya kara da cewa 'Isra'ila' da Saudiyya na ci gaba da kokarin tunzura kasar Amurka ta kawo wa Iran hari, to sai dai kuma wannan kokari na su ya zama aikin baban giwa don a halin yanzu dai al'ummomin yankin suna ganin Amurka ne a matsayin mai bakar aniya.
Bayanai dai na ci gaba da fitowa dangane da alakar da ke tsakanin Saudiyya da haramtacciyar kasar Isra'ilan da kuma hada bakin da suke ci gaba da yi wajen cutar da Iran da kuma haifar da rashin tabbas a yankin Gabas ta tsakiya.