Nov 04, 2017 06:30 UTC
  • Za'a Gudanar Da Bukukuwan 13 Ga Watan Abaan A nan Iran A Garuruwa Fiye Da 1000 Guda.

Yau Asabar ce 13 ga watan Aban na wannan shekara ranar da aka ware a nan Iran, aka kuma bata sunan ranar " yaki da kasashe masu girman kai na duniya".

Ranar 13 ga watan Aban dai tana da munasabobi guda uku a tarihin juyin juya halin musulunci a nan Iran, ranakun sun hada da zagayowar ranar da daliban jami'a a nan Tehran suka shiga ofishin jakadancin kasar Amurka a nan Tehran suka kuma kama dukkan jami'an diblomasiyyar Amurka da ke ciki, suka kuma gano cewa ofishin jakadancin ya zama wani wuri na gudanar da ayyukan leken asirin Amurka a cikin kasar.

Domin raya wadannan ranaku dai za'a gudanar da zanga zanga a garuruwa da birane kimanin 1000 guda a duk fadin kasar, sannan a Tehran yan jaridu kimani 110 ne daga kafafen yada labarai na kasashen waje, sai kuma wasu 500 daga cikin kafafen yada labarai na cikin gida zasu halarci taron da za'a gudanar a kusa da tsohon ofishin jakadancin Amurka da ke Tehran. Inda kuma ake sa-ran Shugaban Majalisar koli ta tsaron kasa Ali Shamkhani zai yi jawabi a taron. 

Tags