Iran Ta Jaddada Wajabcin Janyewar Yahudawan Sahayoniya Daga Yankunan Da Suka Mamaye
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i25369-iran_ta_jaddada_wajabcin_janyewar_yahudawan_sahayoniya_daga_yankunan_da_suka_mamaye
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa kan daukan matakin kawo karshen mamaye yankunan Palasdinawa da yankin tuddan Jolan na kasar Siriya da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke ci gaba da yi.
(last modified 2018-08-22T11:30:57+00:00 )
Nov 08, 2017 06:13 UTC
  • Iran Ta Jaddada Wajabcin Janyewar Yahudawan Sahayoniya Daga Yankunan Da Suka Mamaye

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa kan daukan matakin kawo karshen mamaye yankunan Palasdinawa da yankin tuddan Jolan na kasar Siriya da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke ci gaba da yi.

A jawabinsa a zaman taron kwamitin babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a jiya Talata: Jakadan kasar Iran a Majalisar Dinkin Duniyar Reza Najafi ya yi Allah wadai da ci gaba da mamaye yankunan Palasdinawa da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi. Kamar yadda ya bayyana mamayar da cewa ta yi hannun riga da dokokin kasa da kasa gami da ruhin dan Adamtaka.

Har ila yau jakadan kasar ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan rashin amincewa da ci gaba da mamaye yankin tuddan Jolan na kasar Siriya da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke ci gaba da yi, tare da jaddada wajabcin tilastawa haramtacciyar kasar ta Isra'ila janyewa daga yankin.