Rauhani:Makiya Na Kokarin Kulla Wani Sabon Makirci A Yankin.
Shugaban jamhuriyar musulinci ta iran ya bayyana cewa bayan rashin nasarar makiya game da makircin da suka kulla a yankin yanzu kuma suna kokarin kula wani sabon makirci.
Bayan ganarwarsa da shugaban majalisar musulinci ta Iran da kuma shugaban ma'aikatar shara'a ta kasa, shugaban kasar Iran dakta hasan Rauhahi yayi ishara a game da nasarar da al'ummar yankin suka samu game da yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda a gaban manema labarai inda ya ce a yau al'ummar kasashen Iraki, Siriya da Labnon bisa taimakon dakarun su da kuma goyon bayan kasashe aminnai musaman ma jamhuriyar musulinci ta Iran sun kawar da matsalar da suka fuskanta musaman ma matsalar ta'addanci.
Shugaba Rauhani ya ce shirin makiya na rarraba kasashe bai yi nasara ba, domin haka ganin irin nasarar da kasashen suka samu wajen rusa shirin na makiya ya sanya bacin rai da bakin ciki a cikin zukatan mahukuntan Amurka da Haramtacciyar Kasar Isra'ila.
A yayin da ya koma kan kasar Yemen, shugaba Rauhani ya ce kusan shekaru uku kenan ana yiwa al'ummar kasar ruwan bama-bamai, lamarin da ya sanya cutar kwalara ta bulla a cikin kasar, ga kuma fari da ya mamaye kasar, al'umma na cikin yinwa da tsananin bukatar taimako, amma duk da hakan an rufe iyakokin kasar ta sama, kasa da ruwa, da kuma hakan ya hana a shigar da kayan agaji, wannan abu ne da duk wani dan adam ba zai iya jurewa ba.
Shugaba Rauhani ya kara da cewa yanayin da yankin ke ciki a yau na nuni da cewa makiya na kokarin sake kula wani sabon makirci domin haka ya kamata al'ummar yankin su fahimci hakan, su kuma mahukunta su dauki matakin da ya dace domin karya lagon makiya.