Shugaba Rauhani Ya Isa Yankunan Da Girgizar Kasa Ta Shafa A Kermanshah
(last modified Tue, 14 Nov 2017 11:48:46 GMT )
Nov 14, 2017 11:48 UTC
  • Shugaba Rauhani Ya Isa Yankunan Da Girgizar Kasa Ta Shafa  A Kermanshah

A yau da hantsi ne shugaba Rauhani na Iran ya isa yankin da girgizar kasa ta shafa a cikin Lardin kermanshah da ke yammacin kasar Iran, domin duba halin da al'ummar yankin suke ciki, musaman ma wadanda abin ya shafa.

Bayan isarsa a yankin, shugabab Rauhani ya fara duba mutanen da suka samu raunuka, daga nan kuma ya duba wuraren da girgizar kasar ta yi barna.

Haka nan kuma shugaba Rauhani ya gana da jami'an da suke a wurin musamman na kiwon lafiya da kuma ma'aikatar cikin gidan, kan wajabcin ci gaba da kara bayar da himma wajen bayar da dukkanin taimakon da ya kamata ga al'ummar yankin.

Yanzu haka dai an mayar da wutar lantarki da isakar gas da kuma ruwan sha da suka yanke a wadannan yankuna. Yayin da kuma hukumomin bayar da agaji da na kiwon lafiya da jami'an soji suke ci gaba da taimaka ma mutane.