Jagora Yayi Afuwa Wa Fursunoni Saboda Zagayowar Maulidin Annabi (s)
(last modified Tue, 05 Dec 2017 11:02:47 GMT )
Dec 05, 2017 11:02 UTC
  • Jagora Yayi Afuwa Wa Fursunoni Saboda Zagayowar Maulidin Annabi (s)

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi afuwa ga wasu fursunoni da kuma rage wa'adin zaman gidan yari ga wasu don tunawa da murnar zagayowar Maulidin Manzon Allah (s).

A wata sanarwa da ofishin Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya fitar a yau din nan Talata ya bayyana cewar saboda zagayowar ranar Maulidin Manzon Allah (s) Jagoran juyin juya halin Musuluncin, Ayatullah Khamenei ya amince da bukatar da shugaban Ma'aikatar shari'a kuma alkalin alkalai na Iran Ayatullah Sadeq Amoli Larijani ya gabatar masa na yin afuwa da  kuma rage hukuncin zaman gidan yari da aka yanke wa wasu fursunoni 1700 da suke zaman gidan yari.

A kwanakin baya ne da Ayatullah Larijanin, cikin wata wasika da ya aike wa Jagoran ya bukace shi da yayi afuwa ga wadannan fursunoni don murnar zagayowar ranar haihuwar Ma'aikin Allah (s).

A kowace shekara dai Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kan yi afuwa ko kuma rage wa'adin zaman gidan yarin wasu daga cikin fursunonin da ake tsare da su don nuna farin ciki da ranar haihuwar Fiyayyen Halittan, Manzon Allah Muhammad (s).