An Jinjinawa Kasar Iran Kan Nasarar Da Aka Samu Kan Kungiyar Daesh
Wani sharerren dan jirida a kasar Sudan ya yaba da rawar da kasar Iran ta taka wajen kawo karshen kungiyar yan ta'adda ta Daesh a kasar Iraqi.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Abdul-baqi Al-zzaafir wani sanennen dan jarida a kasar Sudan yana bayyana cewa rawar da kasar Iran da kuma kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon suka taka a kawo karshen kungiyoyin yan ta'adda a kasashen Siria da Iraqi a bin a yaba ne.
Azzaafir ya kara da cewa dole ne kasashen larabawa da musulmi su godewa wadannan mutane don kawo karshen wadan nan kungiyoyi.
Har'ila yau dan jaridar ya kara da cewa yakuwan da kasar saudia take yi na cewa kungiyar hizbullah kungiyar yan ta'addan ne ba gaskiya bani kuma wannan yakuwar ta siyace ce kai babu kanshin gaskiya a cikinta.