Iran Ta Yi Watsi Da Zargin Mikawa 'Yan Houtsi Makami Mai Linzami
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i26355-iran_ta_yi_watsi_da_zargin_mikawa_'yan_houtsi_makami_mai_linzami
Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta yi watsi kwata kwata da zarge-zarge marar tushe da jakadiyar Amurka a MDD, Nikki Haley, ta yi, na cewa makami mai linzamin da 'yan gwagwarmayar neman sauyi na Houtsi a Yemen suka harba zuwa birnin Riyad na kasar Saudiyya, kirar Iran ne.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Dec 15, 2017 04:29 UTC
  • Iran Ta Yi Watsi Da Zargin Mikawa 'Yan Houtsi Makami Mai Linzami

Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta yi watsi kwata kwata da zarge-zarge marar tushe da jakadiyar Amurka a MDD, Nikki Haley, ta yi, na cewa makami mai linzamin da 'yan gwagwarmayar neman sauyi na Houtsi a Yemen suka harba zuwa birnin Riyad na kasar Saudiyya, kirar Iran ne.

Wata sanarwa da tawagar Iran a MDD ta fitar ta ce bayanan marar digi da Haley ta yi kan kasar ''rashin sanin ya kamata ne da kuma tsokana''

Shi ma da yake maida martani kan bayanan na Haley, ministan harkokin wajen kasar ta Iran, Mohammad Jawad Zarif, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa '' a lokacin ina MDD na sha ganin irin wannan wasan kwaikwayo da kuma abin da ya haifar'' 

A jiya ne dai jakadiyar Amurka a MDD ta gabatar da wasu tarkacen makamai wanda ta ce kirar kasar Iran ne ciki har da na wani makami mai linzami wanda Amurkat ta karba daga Saudiyya bayan cafke shi a lokacin da 'yan Houtsi suka harba shi zuwa Riyad a kwanakin baya.

A lokacinda aka tambayi Haley cewa, ko a wanne lokaci aka mika makamin, ta kasa cewa uffan, tana kawai mai dogaro da cewa tarkacen makaman hujja ce da Iran tana keta dokokin kasa da kasa, kana kuma babbar barazana ce ga makobtanta da kuma yankin.

MDD dai ta bayanna cewa kawo yanzu ba ta hujjoji kuma bata kai ga tantance makamin kirar ina ne ba ko kuma suwa ke da shi ba, tana mai cewa tana ci gaba da gudanar da bincike.