Yemen : Iran Ta Musunta Mika Wa 'Yan Houthi Makamai
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i26533-yemen_iran_ta_musunta_mika_wa_'yan_houthi_makamai
Jamhuriya Musulinci ta Iran ta musanta zargin cewa tana mika wa 'yan gwagwarmaya na Houthi a Yemen makaman yaki.
(last modified 2018-08-22T07:01:10+00:00 )
Dec 20, 2017 07:49 UTC
  • Yemen : Iran Ta Musunta Mika Wa 'Yan Houthi Makamai

Jamhuriya Musulinci ta Iran ta musanta zargin cewa tana mika wa 'yan gwagwarmaya na Houthi a Yemen makaman yaki.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen ne Bahram Qasimi, ya bayyana hakan, bayan zargin da Saudiyya da yi na cewa kasar ce ke mika wa 'yan Houthi din na Yemen makamai.

Hakan dai ya biyo bayan harba wani makami mai linzami ne a karo na biyu da 'yan gwagwarmayar na Houthi suka yi zuwa birnin Riyad.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da Iran take musunat zargin kasashen Amurka da Saudiyya na cewa tana mika wa 'yan Houthi din makaman yaki.