Zarif Ya Mayar Da Martani Ga Shugaba Trump Na Amurka
Ministan harakokin wajen jamhoriyar musulinci ta Iran ya yi kakkausar suka a game da munaficin shugaban Amurka kan Al'ummar kasar Iran.
Ministan harakokin wajen jumhoriyar musulinci ta Iran Muhamad Jawad Zarif ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa Shugaban ksar Amurka Donal Trump na amfani da hanya ta ban mamaki wajen bayyana girmawawarsa ta karshe ga al'ummar Iran, daga kiransu 'yan ta'adda, da kuma sanya doka na takaita bulaguronsu zuwa Amurka har zuwa cin mutunci game da sunan Tekun Fasha, sama da wannan, taimakonsu ta hanyar haramta musu hakkokinsu na tattalin arziki bayan yarjejjeniyar da kasar Iran ta cimma tsakanin ta da kasashe biyar masu kujerar din dindin a kwamitin tsaron MDD gami da kasar Jamus game da shirin nukiliyar zaman lafiya na kasar ta Iran.
A cikin 'yan kwanakin nan shugaban kasar Amurka Donal Trump cikin shafinsa na Twitwer ya bayyana goyon bayan sa ga mutanan da suka tayar da hatsaniya a kasar ta Iran.
Zarif ya ce akwai mamaki da mutuman da ya kira al'ummar Iran da 'yan ta'adda jiya kuma a yau shi ne ke bayyana goyon bayansa na munafici ga wadanda suka gudanar da zanga-zangar da ta kai tayar da hatsaniya ta kasar Iran, kuma wani cin mutunci na daban ga al'ummar ta Iran kuma shi ne ya kira da mahalarta zanga-zangar da 'yan yunwa,inda ya ce al'ummar ta Iran dake fama da yunwa al'umma da take bukatar a tausaya masa.