Jagora: Al'ummar Iran Sun Kunyata Amurka, Birtaniyya Da 'Yan Amshin Shatansu
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar cewa al'ummar Iran sun kunyata Amurka, Birtaniyya da sauran 'yan amshin shatansu yayin da suka fito don nuna goyon bayansu ga tsarin Musulunci da kuma yin Allah wadai da masu tada fitina.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana haka ne a yau din nan Talata a wata ganawa da yayi da dubun dubatan mutanen birnin Qum da suka kai masa ziyara don tunawa da zagayowar shekarar yunkurin al'ummar Qum din a lokacin juyin juya halin Musulunci na kasar ta Iran inda ya ce yayin da yake magana kan fitinar baya-bayan da makiya suka kunna a Iran da kuma irin kiyayyar da suke ci gaba da nuna wa Iran kimanin shekaru 40 din da suka gabata ya bayyana cewar: A wannan karon ma al'ummar Iran da dukkanin karfinsu sun isar wa Amurka da Ingila da 'yan amshin shatansu cewa a wannan karon ma kun gaza sannan a nan gaba ba za ku iya cutar da kasar Iran ba.
Har ila yau yayin da yake magana kan yadda masu tada fitinar suka ci gaba da zanga-zanga da kuma kone-kone, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: A lokacin da al'ummar Iran suka fahimci cewa wadannan mutanen ba a shirye suke su kawo karshen wannan fitinar ta su ba, nan take suka fito kan tituna don yin Allah wadai da masu fitinar da kuma barrantar da kansu daga gare su, yana mai ishara da irin fitowar da mutane suka yi a garuruwa daban daban na kasar ta Iran.
Jagoran ya bayyana cewar babu ruwan al'ummar Iran da suka fito don nuna rashin jin dadinsu da matsaloli na rayuwa da suke fuskanta da kuma mutanen da suka yi kone-kone da fadin wasu kalmomi na batanci wadanda suke da alaka da makiyan al'ummar Iran da suke wajen kasar.