An Gargadi Amurka Akan Sakamakon Ficewa Daga Yarjejeniyar Nukiliya Da Iran
(last modified Tue, 09 Jan 2018 19:15:22 GMT )
Jan 09, 2018 19:15 UTC
  • An Gargadi Amurka Akan Sakamakon Ficewa Daga Yarjejeniyar Nukiliya Da Iran

Tsohon ministan makamashi na kasar Amurka, Ernest Moniz ne ya gargadin gwamnatin kasarsa akan abinda zai biyo bayan ficewar Amurka daga cikin yarjejeniyar

Ernest Moniz ya ce matukar Amurkan ta fice daga cikin yarjejeniyar, to za a mai da ita saniyar ware a duniya. Bugu da kari Moniz ya ce; Ficewar Amurkan yana nufi ta ci kasa.

A ranar 13 ga watan Oktoba na 2017 ne dai  shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar ficewar kasarsa daga cikin yarjejeniyar Nukiliya da Iran, tare da mikawa majalisar dokokin kasar ta Congress damar daukar mataki akan hakan.

A tsakiyar wannan watan na janairu ne shugaban kasar ta Amurka zai sake bayyana matsayarsa dangane da  ci gaba da dauke wa Iran takunkumi  a karkashin yarjejeniyar Nukiliya.

Tun da fari, tsoffin sojoji da jami'an diplomasiyya sun gargadi gwamnati Amurka da kada ta fice daga cikin yarjejeniyar.