Larijani: Hadin Kai Tsakanin Kasashen Musulmi Wajbi ne
Shugaban Majalisar dokokin kasar Iran ya ce a yanzu Duniyar musulmi na fama da matsaloli da dama, wanda hadin kai tsakanin kasashen musulmi ne kawai zai magance su.
A yayin da yake ganawa da Salifou Timore mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Burkina Faso a marecen jiya Asabar, shugaban majalisar shawarar musulinci ta kasar Iran Dakta Ali Larijani ya ce taron hadin kai tsakanin al'ummar musulmi dake gudana a kowace shekara a nan birnin Tehran, wata dama ne na cimma ra'ayi guda na fuskantar matsalolin da ake fama da su a yau.
Larijani ya ce a yau Duniya na kallon irin matakin da mahukuntan Amurka ke dauka, kuma matakin mayar da birnin Qudus, hedkwatar haramtacciyar kasar Isr'aila, daya ne daga cikin siyasar Amurka na nuna babbanci a tsakanin al'umma.
A yayin da yake maraba da fadada alaka a tsakanin kasashen biyu,Salifou Timore mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Burkina Faso ya ce kafin ya zo nan birnin Tehran ya gana da jakadan jamhuriyar musulinci ta Iran dake kasar sa kuma sun tattauna kan batutuwa da dama ciki kuwa har da batun buda ofishin jakadancin kasar Burkina Faso a nan birnin Tehran.
Mista Timore ya bayyana damuwarsa kan matakin da shugaban Amurka ya dauka a game da birnin Qudus, inda ya ce wannan mataki nada hadarin gaske ga kasar Amurka kuma ya zama wajibi al'ummar musulmi su kalubalance shi.