An Kai Hari Kan Ma'aikatan Hako Mai A Kudancin Najeriya
Kakakin 'yan sandar jahar Delta da ke kudancin Najeriya ya sanar da kai harin kan wasu ma'aikatan hako danyen man fetur a yankin.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Andrew Aniamaka kakakin 'yan sandar jahar Delta a jiya juma'a na cewa wasu mutane dauke da makammai sun sace ma'aikata biyar na kamfanin hako mai na Sahara Energy Oil Company a karamar hukumar Ajoki da ke iyaka da jihohin Delta da Edo a kudancin kasar.
Mista Aniamaka ya ce lamarin dai ya faru ne tun a yammacin ranar Laraba kuma a halin yanzu ba su da wani cikakken labari kan yadda aka sace wadannan ma'aikata guda biyar, amma kuma tuni sojoji suka baza ma'aikatansu domin gano inda aka kai wadannan ma'aikata.
Sai dai wani mazaunin yankin da ya ganewa idanunsa lamarin, ya ce mutanen da aka sace 'yan Najeriya ne kuma suna cikin jirgin ruwa ne bisa hanyarsu ta zuwa wurin aiki lokacin da wasu mutane guda biyar dauke da makamai fuskokinsu a rufe suka kai musu harin.