Jami'an Tsaron Iran Sun Dakile Wani Makircin Harin Ta'addancin Saudiyya A Kasar
(last modified Thu, 25 Jan 2018 17:41:54 GMT )
Jan 25, 2018 17:41 UTC
  • Jami'an Tsaron Iran Sun Dakile Wani Makircin Harin Ta'addancin Saudiyya A Kasar

Jami'an tsaron kasar Iran sun sanar da kama wasu tarin ababe masu fashewa da kuma wasu bama-bamai masu karfin gaske da wasu 'yan ta'adda da suke samun goyon bayan Saudiyya suke son amfani da su a wajen tarurrukan jama'a a cikin kasar Iran.

A wata sanarwa da Ma'aikatar leken asiri da tattaro bayanan sirri na Iran din ta fitar ta ce jami'an Ma'aikatar sun sami nasarar gano wasu bama-bamai kimanin guda 23 da ake shirin tayar da su daga nesa da nufin tayar da fitina da kai hare-haren ta'addanci a Gabashin kasar ta Iran. Sanarwar ta ce 'yan ta'addan sun sami nasarar shigo da wadannan bama-bamai ne ta kan iyakokin Gabas na kasar Iran din bisa taimakon hukumomin leken asirin kasar Saudiyya.

Har ila yau Ma'aikatar  ta ce jami'anta sun kame wasu ababe masu fashewa tare da sinadaren hada bama-bamai daga wajen wata kungiyar ta'addanci da suke gudanar da ayyukansu a lardin Kordestan na kasar, sai dai kuma Ma'aikatar ba ta yi karin bayani kan wajajen da wadannan 'yan ta'addan suke son kai harin bam, a kokarin da take yi na ci gaba da bincike da kara gano masu wannan bakar aniyar.

Ma'aikatar dai ta ce bincike da ta gudanar ta gano hannun gwamnatin Saudiyya cikin wannan makircin a ci gaba da kokarin da Saudiyyan ta ke yi na dagula lamurran tsaro a cikin kasar Iran kamar yadda Yarima mai jiran gado na Saudiyyan Muhammad bn Salman da kuma ministan harkokin wajen kasar Adel al-Jubeir a fili suka sanar da wannan shiri da suke da shi.

A baya ma dai jami'an tsaron na Iran sun sha kame irin wadannan 'yan kungiyar ta'addancin da suke tabbatar da alakar da suke da ita da kasar Saudiyya.