Rauhani:Gwamnati Za Ta Ci Gaba Da Tsarin Gina Kasa
Shugaban jamhuriyar musulinci ta Iran ya bayyana cewa da taimakon Allah da kuma taimakon al'umma, gwamnati za ta ci gaba da shirinta na kadamar da gine gine tare da raya dukkanin lardunan kasa.
A yayin taron manema labarai na karshen ziyararsa a lardin Kerman, inda ya gana da al'ummar yankin tsaunuka na Kuhban da suka fuskanci girgizar kasa a watanin baya, shugaban jamhuriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rauhani ya bayyana kyakkyawan fatansa na kammala wasu gidaje da aka fara ginawa wadanda za su jure girgizar kasa da gwamnatin take gina wa al'ummar wannan yanki.
Yayin da yake ishara kan halartar al'ummar Iran fagage daban daban na kasar, Shugaba Rauhani ya tabbatar da cewa bayan halartar al'umma a fagen zaben shugabaninsu, su nada damar bayyana ra'ayinsu da kuma bayar da shawarwari kan yadda hukumomin kasar ke gudanar da mulki.
Shugaba Rauhani ya kara da cewa ta hanyar hadin kai al'ummar kasar za ta fita daga cikin mawuyacin halin da take ciki a yau, kuma a cikin shekaru 40 da suka gabata al'ummar kasar ta fita daga cikin matsaloli daban daban tare da samun nasarori masu yawa.
A jiya Alhamis, shugaba Rauhani ya bude wasu manyan ayyuka da gwamnati ta kaddamar a lardin Kerman tare da bayar da umarni na fara gina wasu manyan ayyuka na daban da suka shafi ma'adinai da masana'antu a lardin.