Kakkabo Jirgin Israi'la F-16 : Iran Ta Musunta Yin Kutse
Ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriya Musulinci ta Iran ta yi fatali da zarge-zarge marar digi da mahukuntan yahudawa mamaya na Isra'ila sukayi na cewa ta yi kutse a sararin samaniyar Isra'ila.
Iran ta bakin kakakin ma'aikatar harkokin wajenta, Bahram Qassemi, ta ce bayyanan na Isra'ila, na cewa Iran ta yi mata kutse da wani jirgi marar matuki, kana tana da hannu a kakkabo jirgin yakinta a Siriya wannan faci fadi ne kawai,
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, Bahram Qassemi, ya kara da cewa, Siriya a matsayin ta na 'yantaciyyar kasa, tana da 'yancin kare kanta da kuma maida martani kan duk wani yunkurin na kaddamar mata da hari daga waje.
Iran dai ta kare kasancewarta a Siriya a matsayin bada horo ga dakarun Siriya kuma bisa bukatar mahukuntan Damascos.
A jiya Asabar ne dai makaman kariya na rundunar sojin kasar Siriya suka kakkabo wani jirgin yakin Isra'ila samfurin F-16, a lokacin da yake kai hare-hare a wasu yankunan Siriya dake kusa da iyaka da Labanon.