Sharhi: Hukumar IAEA Ta Ce Iran Tana Mutunta Yarjejeniyar Nukilya
Shugaban Hukumar kula da makamashin nukilya ta duniya Yukiya Amano, ya tabbatar da cewa Iran tana mutunta yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tare da ita da manyan kasashen duniya.
Amano ya sanar da hakan ne a cikin wani rahoto da hukumar ta fitar a jiya daga babban ofishinta da ke birnin Vienna na kasar Austria, inda bayanin ya tabbatar da cewa tun daga lokacin da aka rattaba hannu kan yarjejeniya kan shirin Iran nukiliya a cikin shekara ta 2015, hukumar tana ci gaba da sanya ido a kan shirin na Iran, kuma har ya zuwa yanzu babu wani abu da jami'an hukumar suka shaida wani abu daga bangaren Iran ba, wanda ya saba wa yarjejeniyar.
Wannan dai yana daga cikin irin rahotanni da hukumar take fitarwa lokaci zuwa lokaci dangane da shirin Iran na nukiliya, da kuma bayani kan yadda Iran din take yin aiki da yarjejeniyar da aka cimmawa tare da ita.
Rahoton ya zo ne kwana daya bayan furucin da shugaba Rauhani ya yi, da ke cewa Iran ba za ta taba zama bangaren da zai fara saba wa wannan yarjejeniya ba, matukar dai dukkanin bangarorin da aka cimma yarjejeniyar tare da su suna mutunta ta.
To sai a nata bangaren gwamnatin Amurka karkashin shugabancin Donald Trump, tana kallon wannan yarjejeniyar a matsayin yarjejeniya mafi muni da Amurka ta taba sa hannu a kanta, domin kuwa Trump ya yi imanin cewa wannan ya bai wa Iran damar ci gaba da shirinta na nukiliya ba tare da wata tsangwama ba, duk kuwa da cewa a yanzu ba ta tace sanadarin uranium da ya kai kashi 20%, amma duk da hakan Trump yana yin barazanar ficewar Amurka daga wannan yarjejeniya, wadda gwamnatin Obama tare da sauran manyan kasashen duniya suka kulla tare da Iran.
Kasantuwar yarjejeniyar an kulla ta ne karkashin jagorancin majalisar dinkin duniya, kuam bangarorin yarjejeniyar sun hada da kungiyar tarayyar turai, kasashen Rasha, China, Birtaniya, Faransa, Jamus da kuma ita kanta Amurka, wannan ya sanya batun ya zama wani babban karfen kafa ga Trump a kan wannan batu.
A lokacin da yake yin tsoka a kan wannan batu a jiya Alhamis, jakadan Iran a kasar Birtaniya Hamid Ba'idi Najad ya bayyana cewa; hakika babbar baraka tsakanin Amurka da sauran kawayenta na turai kan batun yarjejeniyar nukiliya da Iran, inda dukkanin kasashen turai gami da Rasha da China suka tsaya kai da fata a kan cewa dole ne a yi aiki da wannan yarjejeniya kamar yadda aka rattaba hannu a kanta.
A halin yanzu dai Trump ya gabatar da sharadinsa, kan cewa dole ne a yi wa yarjejeniyar kwaskwarima kafin Amurka ta ci gaba da yin aiki da ita, dahakan ya hada har da saka batun makaman kariya na ballistic da Iran take mallaka, ta yadda su ma za su zama karkashin kulawar duniya. Amma tuni Iran ta bayyana hakan da cewa zancen wufi ne, domin kuwa hakan ba ya cikin yarjejeniyar, kuma batun makaman kariya hakki na kowace kasa ta mallake su gwargwadon karfinta, a kan hakan Trump ba shi da wannan hurumi.
A halin yanzu dai Trump na fuskantar matsin lamaba daga Isra'ila ta hanyar manyan kungiyoyin yahudawa masu juya tattalin arzikin Amurka da kuma tasiri a siyasarta, kan ya yi watsi da wannan yarjejeniya, abin da masana ke ganin cewa yin hakan kuma zai kara zubar da mutuncin Amurka a idon duniya, hatta a wajen manyan kawayenta na turai, kuma hakan zai sanya Amurka ta zama saniyar ware a cikin lamarin, kamar yadda kuma hakan zai sanya a daina dogaro da ita a kan duk wasu yarjeniyoyi da za ta sanya hannu a kansu kan wasu lamurra a nan gaba, wanda hakan ya sanya Trump da mukarrabansa a cikin wani hali na gaba kura baya sayaki.