Shugaba Rauhani Ya Fara Wata Ziyarar Aiki A Yau A Kasar Turkmenistan
Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya fara gudanar da wata ziyarar aiki a kasar Turkenistan a yau.
Kamfanin dillancin labaran kasar Iran ya baya da rahoton cewa, a ziyarar tasa shugaba Rauhani zai gana da shugaban kasar Turkmenistan Qurban Quli Bardi Muhamaduv, inda za su tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu,a bangarori na tattalin arziki da kasuwanci da kuma saka hannayen jari.
Kafin ya bar birnin Tehran a yau, shugaba Rauhani ya bayyana cewa, a ziyarar tasa a kasar Turkmenistan, za a kafa wata babbar hadaka ta kasuwanci da bunkasa harkokin tattalin arziki tsakanin kasashen biyu, kamar yadda kuma za a sanya hannu kan wasu yarjeniyoyi a bangaren makamashi a tsakaninsu.