Martanin Iran Kan Kasar Saudiya
(last modified Wed, 18 Apr 2018 07:51:48 GMT )
Apr 18, 2018 07:51 UTC
  • Martanin Iran Kan Kasar Saudiya

Kakakin ma'aikatar harkokin kasashen Iran Bahram Qasemi ya yi watsi da zarge-zangen da sarkin saudiya ya yiwa Iran a taron kasashen larabawa karo na 29.

Qasemi ya ce  wasu kasashe  a kan rashin sani har yanzu na ci gaba da kuskuren da suke a kai a game da jamhoriyar musulinci ta Iran, sun manta da manyan makiyan al'ummar musulmi, sannan ya bayyana zarge-zargen da  Sarkin Salman na Saudiya ya yi wa Iran da cewa yunkuri ne na  haifar da gaba a tsakanin Kasashen musulmi ne, kuma hakan  ba maslaha ce gare su ba.

Qasemi ya ce wannan zargi ne na siyasa wanda ba shi da wata kima, amma kuma  a lokaci guda kokari ne na haifar da gaba da fitina  a tsakanin kasashen musulmi, wanda babu abin da irin wanan siyasa za ta haifar illa ci gaba da kara raunana kasashen musulmi.

Ya kara da cewa hakika wannan babar hidima ce ga manyan kasashe masu kiyayya da musulunci, kuma hakan zai kara baiwa makiyan musulmin damar cin Karensu babu babbaka, domin musulmin sun zubar da kimarsu a gaban su.

Har ila yau Bahram Qasemi  ya ce Iran ba ta gaba da wata kasar musulmi, kuma har kullum tana yin kira ne zuwa tattaunawa da fahimtar juna tsakanin musulmi baki daya, tare da samun fahimta da kuma girmama juna, da aikin tare domin ci gaban al'ummar musulmi, maimakon zama 'yan koren kasashe 'yan mulkin mallaka.

A ranar Alhamis din da ta gabata ce aka gudanar da taron kasashen Larabawa karo na 29 a birnin Dammam na kasar Saudiya, inda a yayin taron, sarki Salman  mai shekaru 82 ya  bayyana Iran a matsayin mai shishigi a cikin harkokin cikin gidan kasashen Larabawa da kuma kawo tarnaki cikin lamarun kasahen yankin Gabas ta Tsakiya.

Kakakin m'aikatar harakokin wajen Iran, ya ce wannan zargi da hukumomin saudiyan ke yiwa Iran ba shi ba ne iransa na farko, kuma ba zai kasance na karshe ba,manufar yin hakan kuma shi ne kawar da tunanin musulmi na alakar kasar Saudiya da wasu kasashen Larabawa da Amurka  tare da haramtacciyar kasar Isra'ila, kuma wannan siyasa ta saudiya babu abinda za ta kara aifawarwa al'ummar musulmi face ci gaba da zubar da jini, kamar yadda yake gudana a kasashen Siriya, Iraki, Yemen da kuma Palastinu.

A halin da ake cikin kasar Saudiya ta hade kai da kasar Amurka da Haramtacciyar kasar Isra'ila ana yi wa al'ummar Palastinu kisan kiyashi, kuma ta kafa kawance tana ci gaba da yiwa al'ummar kasar Yemen kisan kare dangi, amma duk da hakan duniya da masu rajin kare hakin bil-adama  sun yi shuru, saboda hakan ya yi daidai da manufar manyan kasashen Duniya,wannan siyasa ita ce kasar Iran ke adawa da ita, kuma ta kan taimakawa duk wani da ake zalinta domin kare kansa, wanda hakan ya sanya hukumomin saudiya ke ganin cewa kasar Iran din na yin shisshigi ga harakokin cikin gida na kasashen Larabawa.