Iran : Jagora Ya Yi Kira Ga Hadin Kan Musulmi
(last modified Fri, 27 Apr 2018 03:36:04 GMT )
Apr 27, 2018 03:36 UTC
  • Iran : Jagora Ya Yi Kira Ga Hadin Kan Musulmi

Jagoran juyin juya halin Musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya yi kira ga wajabcin hadin kan musulmi, a daidai lokacin da a cewarsa manyan kasashen duniya ke kara shishigi a harkokin kasashe, ta hanyar keta huriminsu.

Jagoran na bayyana hakan ne a Jiya Alhamis, a lokacin da yake ganawa da 'yan takara 380 da suka halarci musabakar karatun Al'Qur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a nan Tehran. 

Jagoran ya yi kiran ne bisa la'akari da ayoyin Al'qur'ani mai tsarki dake bukatar hadin kan musulmi, ta yadda zasu tunkari masu girman kai, wanda ya ce Al'Qur'ani ya yi mana gargadi akan rashin hadin kai, wanda kuma shi ne ke hadassa cin hanci da rarrabuwa da kashe kashe.

Jagoran  ya kuma bada misalai da dama, wadanda suka hada da halin da ake ciki a kasar Yemen, inda ya ce walwala da jin dadi da ya kamata a samu sun koma juyayi, haka ma lamarin yake a Afganistan, Pakistan, ko kuma a Siriya, kuma duk wannan na faruwa ne saboda mun yin sakaci da abunda addininmu yake cewa.

A daya bangare Jagoran ya bada misali da irin juriyar da Jamhuriya Musulinci ta Iran ta yi na tsawan shekaru 40 kan barazana da girman kai na mayan kasashen duniya, wanda ya ce babban abun alfahari ne ga kasar.