Shugaba Rauhani Ya Taya Al'ummar Saliyo Murnar Zagayowar Ranar Samun 'Yancin Kasar
(last modified Sat, 28 Apr 2018 17:39:20 GMT )
Apr 28, 2018 17:39 UTC
  • Shugaba Rauhani Ya Taya Al'ummar Saliyo Murnar Zagayowar Ranar Samun 'Yancin Kasar

Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya taya al'ummar kasar Saliyo murnar zagayowar lokacin samun 'yancin kankasar.

Shafin shugaban kasar Iran ya bayar da bayanin cewa, shugaba Rauhani ya aike da sako zuwa ga shugaban kasar Saliyo Julius Bio Maada, inda ya taya shi murna tare da sauran dukkanin al'ummar kasar Saliyo kan zagayowar ranar samun 'yancin kasar daga mulkin mallakar turawan Birtaniya.

Haka nan kuma shugaba Rauhani ya bayyana jin dadinsa dangane da yadda shugaba Maada Bio ya bayyana aniyar ci gaba da kara fadada alaka da kasar Iran dukkanin bangarori, musamman a bangaren kasuwanci, tattalin arziki, da harkokokin ilimi da al'adu.

A ranar 27 ga watan Afrilun shekara ta 1961 ce kasar saliyo ta samun 'yancin kai daga mulkin mallakar turawan Birtaniya.