Yarjejeniyar Nukiliya : Macron Da Rohani Sun Tattauna Ta Wayar Tarho
(last modified Wed, 09 May 2018 16:59:08 GMT )
May 09, 2018 16:59 UTC
  • Yarjejeniyar Nukiliya : Macron Da Rohani Sun Tattauna Ta Wayar Tarho

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da twakwaranasa na Iran Hassan Rohani sun tattauna ta wayar tarho yau Laraba bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran.

Shuwagabannin biyu sun jadadda yin aiki tare don kare yarjejeniyar da manyan kasasshen duniya suka cimma da Iran a shekara 2015, a cewar wata sanarwar fadar ''Elysee''. 

Hakazalika bangarorin biyu sun cimma matsaya guda ta yin aiki tare da du kasashen da suke da bukata don ci gaba da yin aiki da yarjejeniyar da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin, kuma nan bada jimawa ba ministocin harkokin wajen kasashen zasu fara tuntubar juna don fara wannan aikin.

Dama bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar a jiya Talata, kasashen uku na turai da suka hada Faransa, Jamus da Biritaniya wadanda suka sanya wa yarjejeniyar hannu a shekara 2015 sun sha alwashin ci gaba da aiki da ita, tare da kira ga Iran data ci gaba da rike alkawarin data dauka, a yayin da su kuwa zasu ci gaba da dauke mata jerin takunkumi.

Mista Macron ya ce zai tattauba wannan batubn da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin a yayin ganawar da ake sa ran zasuyi a karshen wannan wata.

Amurka dai ta yi wa kasashen turan barazanar takunkumi, muddun kamfanoninsu suka ci gaba da kasuwanci da Iran, batun da Faransa ta ce zata tattauna kan shi tukuru da Amurkar.