IAEA: Iran Tana Yin Aiki Da Yarjejeniyar Nukiliya Kamar Yadda Ya Kamata
(last modified Fri, 11 May 2018 02:30:57 GMT )
May 11, 2018 02:30 UTC
  • IAEA: Iran Tana Yin Aiki Da Yarjejeniyar Nukiliya Kamar Yadda Ya Kamata

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta fitar da sanarwa da ke tabbatar da cewa Iran tana yin aiki daidai da yarjejeniyar da aka cimmawa tare da ita da manyan kasahen duniya.

A cikin bayanin da hukumar ta IAEA ta fitar, ta bayyana cewa tun bayan da aka cimma yarjejeniyar nukiliya tare da Iran a cikin cikin shekara ta 2015 ya zuwa yanzu, babu wani wuri da Iran ta saba wa wannan yarjejeniyar, a kan hukumar zata ci gaba da yin aiki da wannan yarjejeniya kamar yadda aka rattaba hannu a kanta.

Hukumar IAEA dai ita kadai ce take da hakkin sanya ido a kan shirin na Iran, kuma ita kadai ce bisa dokar majalisar dinkin duniya, take da hakkin ta yi bayani a kan ko Iran tana yin aiki da yarjejeniyar ko ba ta yin aiki da ita.

Wannan rahoto na hukumar IAEA ya kara fallasa Donald Trump a idon duniya, wanda ya fice daga wannan yarjejeniya bisa hujjar cewa Iran ba ta yin aiki da yarjejeniyar, wanda kuma rahoton hukumar IAEA shi ne abin da majalisar dinkin duniya za ta yi aiki da shi.