Rasha : Putin Ya Gana Da Shugaban Hukumar IAEA
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya gana da shugaban hukumar kula da harkokin makamashin Nukliya ta duniya Yokiyo Amano a birnin Mosco inda ya jaddada matsayin kasar Rasha na mutunta yerjejeniyar shirin Nukliyar kasar Iran.
Kamfanin dillancin labaran Interfax na kasar Rasha ya nakalto ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha tana fadar haka a yau litinin ta kuma kara da cewa shugaba Putin ya bayyana damuwarsa kan matakin da gwamnatin kasar Amurka ta dauka na ficewar daga yerjejeniyar shirin Nukliyar kasar Iran, ya kuma tabbatar da cewa Rasha tana son ci gaba da mutunta yerjejeniyar.
A nashi bangaren shugaban hukumar IAEA ya kara jaddada cewa kasar Iran tana rike da alkawarin da ta dauka na yerjejeniyar shirin nukliyar kasar, bata taba sabawa ko da guda daga cikinsu ba.