Hukumar Tarayyar Turai Ta Sanar Da Goyon Bayan Yarjejeniyar Nukiliyar Iran
(last modified Sat, 19 May 2018 17:53:26 GMT )
May 19, 2018 17:53 UTC
  • Hukumar Tarayyar Turai Ta Sanar Da Goyon Bayan Yarjejeniyar Nukiliyar Iran

Hukumar kungiyar Tarayyar Turai, cikin wata sanarwa da ta fitar, ta bayyana goyon bayanta ga ci gaba da kiyaye yarjejeniyar nukiliyan da Iran ta cimma da wasu manyan kasashen duniya a shekara ta 2015.

Kamfanin dillancin labaran Fars na Iran ya bayyana cewar, hukumar Tarayyar Turai din ta bayyana hakan ne bayan wata ganawa da ta hada Kwamishinan makamashi na Turai din Miguel Arias Cañete da shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasar Iran Dakta Ali Akbar Salehi a yau din nan Asabar.

Sanarwar ta bayyana cewar ganawar da jami'an biyu suka yi wani lamari ne da ke nuni da riko da yarjejeniyar nukiliyan da hukumar Tarayyar Turai din da kuma hukumar kula da makamashin nukiliya na Iran suka yi, tana mai cewa hukumar Tarayyar Turai din ta yi amanna da cewa ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar nukiliyan kamar yadda take wani lamari ne da zai taimaka wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyar duniya.

A yau ne dai Mr.  Cañete ya iso Tehran don tabbatar da shirin kungiyar Tarayyar Turai din na girmama yarjejeniyar nukiliyan duk kuwa da ficewar Amurka daga cikinta.