Amurka Ta Dorawa Iran Wasu Karin Takunkumai.
(last modified Thu, 24 May 2018 19:13:03 GMT )
May 24, 2018 19:13 UTC
  • Amurka Ta Dorawa Iran Wasu Karin Takunkumai.

Ma'aikatar kudi ko baitul Malin Amurka ta bada sanarwan karin wasu takunkumai a kan Iran wadanda suka hada da kamfanonin jiragen sama na kasar da kuma wasu yan kasuwa.

Kamfanin dillancin labaran "Al-Mayadeen" ya nakalto ma'aikatar kudin tana bada wannan sanarwan a yau Alhamis. Ta kuma kara da cewa takunkumin ya hada da kamfanonin  jiragen sama na Mahon Air da kuma Miraj Air duk na kasar ta Iran da kuma wasu kamfanonin kasar Turkiya wadanda suke aiki tare da wadanan kamfanonin. 

Ma'aikatar ta kara da cewa takunkumin ya hada da yan kasuwan Iraniyawa biyu da kuma daya dan kasar Turkia. Wannan dai shi ne karo na biyu kenan wadanda gwamnatin kasar Amurka take bada sanarwan dorawa kasar Iran Takunkumai tun bayan ficewar kasar daga yerjejeniyar shirin Nukliyar kasar Iran a farkon wannan watan. A wannan karon takunkuman sun hada da da Waliyullah Saif shugaban babban bankin kasar Iran. 

A zagaye na farko na takunkuman dai, Amurkan ta dora takunkuman a kan mutane 6 da kuma kamafanoni ukku ne.