Faransa Ta Soki Kasar Amurka Saboda Siyasarta Akan Iran
Ministan kudi na kasar FaransaBruno Le Maire ya ce; Har yanzu Faransa ba ta karbi jawabi daga Amurka ba dangane da bukatar da ta aike tare sauran kasashen turai na neman kada a sa wa kamfanoninsu masu aiki a Iran takunkumi
Ministan kudin na Faransa Bruno Le Maire ya kara da cewa; Kamfanonin turai suna cikin damuwa kada takunkumin Amurka ya shafe su amma abin takaici har yanzu ba su sami jawabi daga Amurka ba.
Le Maire ya bayyana takaicinsa akan ficewar Amurka daga yarjejeniyar Nukiliya da Iran sannan ya kara da cewa: Ba abu ne da za a laminta da shi ba, Amurka ta nada kanta 'yarn sandar tattalin arziki ta duniya, kuma kuskure ne babba, wanda zai iya kawo rashin zaman lafiya a duniya.
Bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar Nukiliya da Iran, fadar mulkin Faransa ta snar da cewa za ta yi dukkanin abin da za ta iya domin kare kamfanoninta na tattalin arziki a cikin Iran.