Iran : Rohani Ya Fara Wata Ziyara A Turai
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i32160-iran_rohani_ya_fara_wata_ziyara_a_turai
Shugaba Hassan Rohani, na Jamhuriya Musulinci ta Iran, ya fara wata ziyara a nahiyar Turai, wacce za ta kai shi a kasashen Switzerland da Austria.
(last modified 2018-08-22T11:32:03+00:00 )
Jul 02, 2018 10:46 UTC
  • Iran : Rohani Ya Fara Wata Ziyara A Turai

Shugaba Hassan Rohani, na Jamhuriya Musulinci ta Iran, ya fara wata ziyara a nahiyar Turai, wacce za ta kai shi a kasashen Switzerland da Austria.

Wannan ziyarar dai na da manufar kara karfafa alaka da kasashen, da kuma tattauna makomar yarjejeniyar nukiliyar Iran,  bayan ficewar Amurka daga cikinta.

Jim kadan kafin tashinsa, Shugaba Rohani ya bayyana cewa ziyarar tana da matukar mahimmanci, don za ta bada damar fahimtar juna da kasashen turan, kan yarjejeniyar da kuma makomarta, tsakanin kasashen Turan da Iran.