Iran Da Rasha Sun Rattaba Hannu Kan Sabbin Yarjeniyoyi Na Tattalin Arziki
Kasashen Iran da Rasha sun rattaba hannu kan wasu sabbin yarjeniyoyi na kara bunkasa harkokin tattalin arzikia tsakaninsu, musamman a bangaren hada-hadar kudade da kuma harkokin banki.
A jiya Alhamis ne manyan tawagogin kasashen biyu a bangarorin tattalin arziki suka fara gudanar da zama na hadin gwiwa a birnin Tehran na kasar Iran, da nufin kara bunkasa dukkanin harkokin tattalin arziki a tsakaninsu.
Wannan zama ya zo ne a daidai lokacin da Amurka take ta kara matsa lamba a kan kasar Iran domin ganin ta yi wa kasar illa ta fuskar tattalin arziki, domin tabbatar da cewa ta biya bukatun wasu kasashen yankin gabas ta tsakiya da suka zuba mata biliyoyin daloli domin aiwatar da wannan manufa a kan kasar ta Iran.
Gwamnan babban bankin kasar rasha ya ce, za su karfafa hulda tsakaninsu da bababn bankin Iran ta hanyar musayar kudade tsakanin kasashen biyu.