Shugaba Rauhani: Takunkumin Amurka Ba Zai Iya Karya Lagon Iran Ba
A wata zantawa da da ya yi a daren jiya da tashar talabijin ta daya ta kasar Iran, shugaban kasar ta Iran Hassan Rauhani ya bayyana takunkumin da Trump ya kakaba wa kasar da cewa, ba zai iya karya lagon Iran ko durkusar da tattalin arzikinta ba.
Shugaba Rauhani ya ce, Ficewar Trump daga yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tare da Iran, wadda dukkanin kasashen duniya suka amince da ita, tare da fitar da kudirin majalisar dinkin duniya a kanta, hakan yana a matsayin yin fatali ne da ka'idoji na kasa da kasa, wanda kuma Amurka ce ta zama saniyar ware kan wannan batu ba kasar Iran ba.
Ya ce babu ma'ana dangane da kiran da Trump ya yi masa na su tattauna a lokacin da kasarsa take a karkashin takunkumin Amurka, a maimakon hakan da zai fi dacewa ga Trump ya sake yin nazari kan siyasarsa dangane da Iran kan maslahar Amurka, domin abin da ya yi ba maslaha ce ga kasar Amurka ba.
Rauhani ya ce dukkanin kasashen da suke cikin yarjejeniyar nukiliya tare da Iran suna nan a kan bakansu, kuma sun sha alwashin yin fatali da duk wani mataki da Amurka za ta dauka a kan Iran dangane da takunkumin karya tattalin arziki, da hakan ya hada da kungiyar tarayyar turai da kuma kasashen China da Rasha.
Dangane da alakar Iran da sauran kasashe makwabta kuwa, Rauhani ya bayyana cewa Iran ba ta da wata matsala da wata kasa, duk kuwa da cewa wasu 'yan tsirarun kasashe da ba su wuce biyu ko uku ba sun daukar wa kansu tsananin gaba da Iran, amma duk da hakan Iran a shirye take ta tattauna da su domin a warware duk wani sabani ko rashin fahimta, domin ci gaban al'ummomin kasashensu, da kuma kara tattabar da hadin kai tsakanin al'ummar musulmi.
A lokacin da yake amsa tambaya kan matsaloli a bangaren harkoki na tattalin arziki kuwa, Rauhani ya bayyana cewa kasar Iran kasa ce wadda ta dogara da kanta a mafi yawan lamurra da take bukata, saboda haka matsalar da aka fuskanta a cikin 'yan lokutan nan tana da alaka ne da takunkumin da Trump ya sanar a kan kasar Iran, kuma tuni aka dauki matakai na fuskantar lamarin, inda a yau Talata za a fara aiwatar da sabon tsari kan kudaden ketare, wanda zuwa mako mai zuwa za a shiga yin aiki da shi gadan-gadan a dukkanin fadin kasar.
Rauhani ya ce wanann sabon tsarin zai taimaka wajen saukar da farashin dalar Amurka da sauran kudaden waje a kasar Iran, kamar yadda hakan zai bayar da dama ga masu bukatar kudaden su same su a cikin sauki, kamar yadda kuma 'yan kasuwa masu sayen kaya daga waje su ma za su iya samun kudin cikin sauki domin shigo da kaya, kuma za su same su a kan farashi na gwamnati, kamar yadda aka tanadi matakai na sanya ido matuka domin tabbatar da cewa an yi amfani da tsarin, tare da daukar matakai na shari'a a kan duk wanda ya saba ma hakan.
Daga karshe Rauhani ya kara jaddada kira ga dukkanin al'ummar kasar da su zama tsintsiya daya madaurinki daya domin fuskantar duk wani kalubale a kan kasarsu.