Kasashen Iran Da Rasha Sun Jaddada Aiki Tare Don Fada Da Ta'addanci
Aug 10, 2018 06:31 UTC
Jami'an diplomasiyyar kasashen Iran da Rasha da su ka gana da juna sun jaddawa wajabci fada da ayyukan ta'addanci a karkashin Majalisar Dinkin Duniya
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da dokokin kasa da kasa, Gulam Husain Dahqani, ne ya gana da Oleg Syromolotov wanda shi ne jami'i mai kula da ayyukan ta'addanci a ma'aikatar harkokin wajen Rasha, sun jaddada aiki tare a tsakanin kasashensu a wannan fage.
Kasashen biyu suna aiki tare a fagen fada da ayyukan ta'addanci a kasar Rasha da kuma musayar bayanai a kan batun.
Tags