Shugaban Kasar Rasha Zai Kawo Ziyarar Aiki A Nan Tehran
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai kawo ziyarar aiki a nan Iran a ranar Jumma'a 7 ga watan Satumba da muke ciki.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar fadar Krimlin tana fadar haka a jiya litinin. Sannan ta kara da cewa shugaban zai halarci taro shuwagabannin kasashe uku wadanda suke kula da al-amura na yaki da ta'addanci a kasar Siriya ne, wadanda suka hada da shugaba Ruhani na Iran, Rajab Tayyib Urdugan na Turkiya da kuma Shi Putin na kasar Rasha.
Anasa ran shuwagabannin zasu tattauna batun hanyoyin kawo karshen ayyukan ta'addanci a yankin da kuma batun komawar yan gudun hijirar siriya kasarsu.
An gudanar da taron farko na suwagabannin uku a ranar a ranar 22 ga wtan Nuwamban shekara ta 2017 a birnin Suchi na kasar Rasha, na biyu kuma a birnin Ankara na kasar Turkiya a ranar 4 ga watan Afrilu na wannan shekara. Taron tehran shi ne na ukku.