Iran Za Ta Maida Martani Mai Tsanani Bayan Harin Ta'addancin Ahwaz
(last modified Sat, 22 Sep 2018 15:49:22 GMT )
Sep 22, 2018 15:49 UTC
  • Iran Za Ta Maida Martani Mai Tsanani Bayan Harin Ta'addancin Ahwaz

Shugaban Kasar Iran, Hassan Ruhani, ya bayyana cewa Jamhuriya Musulinci ta Iran za ta maida martani mai tsanani bayan harin ta'addancin da aka kai kan faretin sojoji yau Asabar a garin Ahwaz dake yankin Khouzistan a kudu maso yammacin kasar.

Wata sanarwa da ofishin shugaban kasar ya fitar, ta ce Iran ba zata lamunta da duk wani yanayi da zai kasance barazana gare ta ba.

Dakta Ruhani, ya kuma baiwa ma'aikatar leken asirin kasar da kuma duk sauren jami'an tsaron kasar umurnin tantance 'yan ta'addan don gano duk wadanda ke da hannu a harin.

A daya bangaren kuma shugaban kasar, ya isar da sakon ta'aziyarsa ga iyalen wadanda lamarin ya rusa dasu da kuma fatan samun sauki ga wadanda suka raunana.

Shugaban kasar ta Iran ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da ministan cikin kasar da kuma gwamnan yankin na Khousistan.

Kawo yanzu dai mutane 29 ne sukayi shahada a harin, a yayin da 57 suka raunana, kamar yadda, Mojtaba Zolnuri, mamba a kwamitin 'yan majalisar dokoki mai kula da harkokin tsaro kasa da kuma harkokin waje, ya shaidawa tashar talabijin ta larabci mallakin Iran (Al'alam).