Jagora Yayi Kakkausar Suka Ga 'Munafuncin' Kasashen Yammaci Kan Makaman Nukiliya
Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi kakkausar suka munafunci da siyasar harshen damon da kasashen yammaci suke yi dangane da batun amfani da makaman nukiliya, yana mai tunatar da su irin goyon bayan da suka ba wa tsohon shugaban kasar Iraki, Saddam Husseini a yayin da ya kallafa wa Iran a shekarun 1980.
Jagoran juyin juya halin ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da wasu gungun kwamandojin lokacin kallafaffen yaki, tsoffin sojoji da marubuta da mawaka a ci gaba da bukukuwan makon kariya don tunawa da zagayowar shekarar da aka kallafawa Iran din yaki na shekaru 8, inda ya ce duk da irin ihuce-ihucen da kasashen yammacin suke yi dangane da amfani da makamin nukiliya, to amma duk da haka sun ba wa Saddam makamai masu guba wanda yayi amfani da su ba wai kawai a fagen daga ba, face har ma da wasu garuruwa a kan fararen hula.
Ayatullah Khamenei ya ce a wadanda shekarun Iran tana karkashin takunkumi na tattalin arziki da siyasa, kana kuma an hana muryoyin al'ummar Iran su isa ga sauran al'ummomin duniya don su san hakikanin me ke faruwa, don kuwa kafafen watsa labaran ma suna karkashin ikon sahyoniyawa ne.
Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce an hana Iran hatta damar amfani da wasu abubuwa da take bukata, a daidai lokacin da aka ba wa daya bangaren, wato gwamnatin IRaki dukkanin makamai na zamani da take bukata ciki kuwa har da makamai masu guba.