Oct 11, 2018 12:18 UTC
  • Jagora : Babu Wata Matsala Da Ba Za A Iya Warware Ta Ba A Iran

Jagoran juyin musulunci na Iran, Ayatullah Sayiyd Ali Khamnei ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da jami'an gwamnati da ma'aikatar shari'a da kuma 'yan Majalisa.

Ayatullah Sayydi Ali Khamnei ya jinjinawa yadda kwamitin tattalin arziki wanda ya kunshi bangarorin gwamnati, Majalisar shawara da kuma ma'aikatar shari'a, akan yadda yake gudanar da aikinsa.

Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma gabatar da nasihohi ga kwamitin domin fuskantar kalubalen tattalin arziki.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya ci gaba da cewa; Wajibi ne a dauki tsauraran matakai domin warware matsalolin hauhawar farashin kayan masarufi, samar da aikin yi,da kuma tsarin da yake tafiyar da Bankuna.

Wani bangare na jawabin jagoran juyin musuluncin na Iran ya kunshi ishara da takunkumin tattalin arziki da Amurka ta kakabawa Iran yana mai cewa; Matakan da za a dauka na warware matsaloli su zama wadanda za su sa makiya su yanke kauna da cewa za su iya yin tasiri akan Iran.

 

Tags