Iran Ta Taya Al'ummar Brazil Murnar Zaben Shugaban Kasa
(last modified Mon, 29 Oct 2018 18:03:30 GMT )
Oct 29, 2018 18:03 UTC
  • Iran Ta Taya Al'ummar Brazil Murnar Zaben Shugaban Kasa

Kakakin ma'aikatar harakokin wajen Iran ya taya al'ummar kasar Brazil murnar gudanar da zabe cikin nasara da kuma zaben sabon shugaban kasa.

Al'ummar kasar Brazil, dan takarar jam'iyyar masu tsattauran ra'ayi da kyamar baki Jair Bolsonaro ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a Lahadi bayan da ya samu kaso 55,13 daga cikin dari a yayin da abokin hamayyarsa Fernando Haddad ya samu kaso 44,87 daga cikin dari na kuri'un da aka kada. 

Dubban magoya bayan Bolsonaron sun shafe tsawon dare suna gudanar da shagulgulan murna da wasan wuta a biranen kasar da dama.

Cikin sanarwar da ya fitar a wannan Litinin, kakakin ma'aikatar harakokin wajen kasar Iran Bahram Qaseemi ya ce yadda Al'ummar kasar suka fito wajen zaben sabon shugaban kasar, abin a yaba ne, sannan kuma ya yiwa sabon shugaban kasar fatan alheri.

A yayin da yake ishara kan dadaddiyar alakar dake tsakanin kasashen Iran da Brazil, Bahram Qaseemi ya bayyana fatansa na dorewa tare da bunkasa alakar   a bangarorin siyasa  da tattalin arziki tareda sabuwar gwamnati.