WHO Ta Girmama Iran Saboda Fada Da Cutar Malaria
Babban jami'i a hukumar lafiya mai sa ido akan cutar cizon Sauro Pedro Alonso ya jinjinawa Iran akan yadda take maganin cutar malaria.
Jami'in mai sa ido akan cutar ta cizon sauro a hukumar lafiya ta duniya, ya gana da ministan lafiya na Iran Ali Reza Risy a yau juma'a a birnin Geneva, inda ya bayyana cewa: Rahoton da su ke da shi ya nuna cewa a cikin shekarar 2017 da ta wuce an sami mutane 57 ne kacal da su ka kamu da zazzabin Malaria aduk fadin Iran, wanda yake nuni da koma baya sosai idan aka kwatanta da na shekarar 2000 da aka samu mutane 12,000 da su ka kamu da zazzabin.
A nashi gefen ministan lafiya na Iran ya yi ishara da shirin kiwon lafiya na baya-baya da Iran din ta fito da shi,wanda ya taimaka matuka wajen raguwar masu kamuwa da zazzabin na Malaria.