Shirin Karfafa Taimakekkeniya A Fagen Al'adu Tsakanin Kasar Iran Da Fadar Vatican
Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Fadar Vatican ta darikar katolika ta mabiya addinin kirista sun jaddada bukatar karfafa alakar da ke tsakaninsu musamman a fagen bunkasa harkar al'adu.
A zantawar da ta gudana tsakanin ministan al'adu a fadar Vatican Cadinal Gianfranco Ravasi da jakadan kasar Iran a fadar ta Vatican Sayyid Taha Hashimi a jiya Laraba: Jami'an biyu sun jaddada bukatar karfafa alaka a tsakanin Iran da fadar Vatican tare da bunkasa alakar a fuskar al'adu da taimakekkeniya a harkar ilimin jami'a.
Cadinal Ravasi ya kuma jaddada cewa: Iran tana da dadaddun al'adu da suka samo asali tsawon dubban shekaru, kuma irin wadannan al'adu suna daga cikin dalilan da suka daukaka al'ummar Iran da kara musu kima a idon duniya.
A nashi bangaren jakadan kasar Iran a fadar ta Vatican Sayyid Taha Hashimi ya bayyana shirin Iran na gudanar da makon baje kolin fina-finai da suka shafi addini da al'adun Iran a fadar ta Vatican.