Larijani: Har Yanzu Iran Tana Da Hakkin Ficewa Daga Yarjejeniyar Nukiliya
Shugaban majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran, Dakta Ali Larijani ya bayyana cewar har ya zuwa yanzu Iran tana da hakkin ficewa daga yarjejeniyar nukiliyan da ta cimma da manyan kasashen duniya matukar dai ba a kare mata manufofinta ba.
Dakta Larijani ya bayyana hakan ne a yau din nan Litinin a wata ganawa da yayi da manema labarai inda yayin da yake magana kan yarjejeniyar nukiliyan da kuma ci gaba da tattaunawar da Iran take yi da kasashen Turai ya bayyana cewar: Wajibi ne kasashen Turai su tsai da shawara guda kan yanayin yadda za a gudanar da musayen kudi na kasuwanci tsakanin Iran da kasashen duniya.
Shugaban majalisar shawarar Musulunci na Iran din ya ci gaba da cewa: Matukar dai ba a cimma matsaya guda ba tsakanin Iran da Turawan kan wannan batu, to kuwa Iran za ta dau matsaya kan ci gaba da zama cikin yarjejeniyar ta nukiliya. Yana mai cewa Iran tana da dukkanin hakkin ficewa daga yarjejeniyar matukar dai ba a lamunce mata manufofinta ba.
Dangane da batun sake zama teburin tattaunawa da Amurkan kan wannan batu na nukiliya kuwa kamar yadda shugaban Amurkan ya gabatar, Dakta Larijani ya ce a halin yanzu dai babu wani dalilin da Iran za ta sake zama da Amurka kan wannan batun, yana mai cewa matukar dai Amurka tana son sake zama da Iran a teburin tattaunawa to wajibi ne ta dawo cikin yarjejeniyar da ta fice kana kuma ta tabbatar da kyakkyawar aniyarta kan hakan.