Iran Ta Ki Amincewa Da Batun Rage Yawan Man Da Take Fitarwa
(last modified Fri, 07 Dec 2018 08:58:00 GMT )
Dec 07, 2018 08:58 UTC
  • Iran Ta Ki Amincewa Da Batun Rage Yawan Man Da Take Fitarwa

Ministan man fetur na kasar Iran Namdar Zangeneh ya bayyana cewar a halin da ake ciki Iran ba za ta taba amincewa da rage yawan man fetur din da take fitarwa a kowace rana ba.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar  Iran ya bayyana cewar ministan man fetur na Iran din ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta bayan fage da yayi da tashar talabijin ta CNBC ta Amurka bayan fagen taron kungiyar kasashen masu arzikin man fetur na duniya OPEC da aka gudanar a birnin Vienna na kasar  Austria inda ya ce: Tsawon watannin da suka gabata, Iran ba ta fitar da mai mai yawa ba, don haka ba hakki ne a kanta ta  samo mafitar matsalar da ake ciki ba.

Mr. Zangeneh ya ce kasashen da suka fitar da mai sama da yadda ya kamata ne suke da  alhakin magance matsalar da ta kunno kai a kasuwar man fetur din. Babu wani abin da Iran za ta iya a wannan fagen, yana mai cewa batun rashin yawan mai da Iran take fitarwa wani lamari ne da ba za a taba amincewa da shi ba.

A jiya ne dai membobin kungiyar ta OPEC suka gudanar da taronsu na 175 na tsawon sa'oi 7 ba tare da sun cimma matsaya ba kan batun rage yawan man da ake fitarwa inda za su ci gaba da tattauanwar a yau Juma'a.