Nijar Ta Sanar Da Shirin Shimfida Bututun Mai Zuwa Chadi
Jamhuriya Nijar ta sanar da wani shirinta ta shinfida bututun mai da zai dinga kai manta zuwa kasar Kamaru ta cikin Chadi domin fitar da shi zuwa kasuwannin duniya.
Gwamnatin ta Nijar ta bakin ministan man fetur din ta, Fumakay Gado ta ce, ana sa ran fara aikin a karshen wannan shekara ta 2018.
Domin kara yawan man da take fitar wa, kasar ta Nijar ta cimma wata yarjejeniya hako mai ta biyu da kamfanin man CNPC na China, a yankin Agadem dake kudu maso gabashin kasar.
Wannan dai idan ya tabbata, Jamhuriyar Nijar za ta dinga fitar da mai ganga dari da goma (110,000) ko wacce rana, sabanin ganga 20,000 da take fitar wa yanzu haka.
A shekara 2011 ne kasar ta Nijar mai arzikin karfen urenium da kuma zinari, ta shiga sahun kananen kasashe masu fitar da man fetur, saidai a watan Oktoba na bara, kungiyar nan ta kasa da kasa (EITI), dake sa ido da kuma fafatukar ganin arzikin da ake hakowa a karkashin kasa ya amfani talaka, ta dakatar da Nijar daga cikin tsarin, kan rashin bada haske akan yarjeniyoyin da take kulawa da kuma kason da ya kamata a ware wa jama'ar da ake tono ma'adunan karkashin kasa a yankunansu.
Saidai a matsayin maida martani gwamnatin ta Nijar ta janye kwata kwata daga tsarin na (Extractive Industries Transparency Initiative).