Zarif: Babu Batun Wata Sabuwar Tattaunawa Tsakanin Amurka Da Iran
Ministan harkokin wajen kasar Iran Dr. Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, babu wani batun wata sabuwar tattaunawa a halin yanzu tsakanin kasar Iran da kuma Amurka.
Zarif ya bayyana hakan ne a jiya a taron Doha, inda ya tabbatar da cewa Iran ba a shirye take ta shiga duk wata tattaunawa tare da Amurka ba a halin yanzu, har sai Amurka ta koma cikin yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya wanda ta fice daga cikin yarjejeniyar ba tare da wani dalili ba, domin kuwa hakan yana matsayin yin fatali ne da kudirin majlaisa dinkin duniya kan shirin na Iran.
Dangane da batun yunkurin da Amurka take yi na neman ganin an saka batun makaman Ballastic da Iran take mallaka a cikin yarjejeniyar nukiliya kuwa, Zarif ya ce babu inda aka ambaci hakan a cikin wannan yarjejeniya.
A lokacin da aka tambaye kan zargin da Amurka take yi wa kasar Iran na shiga cikin harkokin kasashen yankin gabas ta tsakiya kuwa, Zarif ya amsa da cewa; Iran daya ce daga cikin kasashen yankin gabas ta tsakiya, saboda haka maganar cewa tana shiga cikin harkokin yankin gabas ta tsakiya ma bai taso, yayin da Amurka kuwa ba ta da wata alaka ko nasaba ta tarihi da ya hada ta da gabas ta tsakiya, amma a halin yanzu ita ce wuka ita ce nama a cikin dukkanin harkokin gabas ta tsakiya, baya ga haka kuma duk wata kasa a yankin da Iran ta tura dakarunta ko masu bayar da shawara kan harkokin soji, to tabbas wannan kasar ce da kanta ta nemi alfarmar hakan daga Iran, shin ita ma Amurka haka ne? ya ce a nan sai mutane su yi hukunci wane ne yake yin shigar shugula a cikin harkokin yankin gabas ta tsakiya.
Dangane da batun kyautata alaka tsakanin Iran da Saudiyya kuwa, Zarif ya ce, har kullum Iran a shirye take ta hada kai da Saudiyya domin samun fahimtar juna da kuma tunkarar matsalolin da suke ci ma musulmi tuwo a kwarya a duniya domin warware su, amma Saudiyya ba a shirye take ta amince da hakan ba, maimakon hakan ma tafi son ganin ana ci gaba da yin rikici da sabani a tsakaninta da sauran kasashen yankin, domin rikicin Saudiyya bai takaita da kasar Iran ba kawai, tana rikici da Syria, Iraki, Yemen, Qatar, kuma kowa ya ga yadda ta tsare Firayi ministan kasar Lebanon Sa'ad Hariri na tsawon kwanaki daga ya kai ziyarar aiki a kasar.