Iran: Dangantaka Tsakanin Kasashen Iran Da Iraqi Tana Da Kyau
(last modified Mon, 17 Dec 2018 19:17:27 GMT )
Dec 17, 2018 19:17 UTC
  • Iran: Dangantaka Tsakanin Kasashen Iran Da Iraqi Tana Da Kyau

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasimi ya bayyana cewa dangantakar tattalin arziki tsakanin kasar Iran da kuma Iraqi tana tafiya kamar yadda ya dace duk tare da matsin lamaba wanda gwamnatin Amurka takewa kasar Iraqi.

Qasimi ya kara da cewa gwamnatin Amurka bata isa ta lalata dangantakan tattalin arziki tsakanin kasashen biyu ba. Dangane da tafiyar Ministan harkokin wajen kasar Iran zuwa kasar Qatar kuma Qasim ya ce siyasar harkokin waje na kasar Iran bata sauya ba, An gina tsarin diblomasiyyar kasar ne kan mutunta juna da kuma musayar ra'ayi da fahinta. Kan wannan tsarin ne gwamnatin kasar Iran take hulada da dukkan kasashen yankin gabas ta tsakiya. 

Sai kuma dangane da labaran da ke cewa wasu kamfanonin kasashen Rasha da Cana sun janye daga kasar Iran Qasimi ya ce wannan labarin ba gaskiya bane, kuma yakamata kafafen yada labarai su dauki irin wadannan labarai daga kafafen da suka dace kafin su yadasu.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen ya yi wannan jawabai ne a taro da yan jaridu na ciki da kasshen waje da ya sabi yi a ko wani mako ma'aikatar.