Kasar Kuwait Za Ta Sake Bude Ofishin Jakadancinta A Kasar Siriya
Gwamnatin kasar Kuwait zata sake bude ofishin jakadancinta a kasar Siriya
Jaridar Al-Watan da kasar Siriya ta nakalto jaridar Al-Qubus ta kasar Kuwait tana fadar haka a bugunta na yau Lahadi. Kasar Kuwait dai ita ce kasa ta ukku daga kasashen larabawa da zata sake bude ofishin jakadancinta a kasar Siriya bayan Bahrain da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.
Kafin haka dai kimani shekaru 8 da suka gabata ne kasashen Larabawa suka yi ta rige-rige na rufe ofisoshin jakadancinsu a birnin damascus bayan makircin da wasu kasashen na larabawa da kuma kasashen yamma suka kulla na kifar da gwamnatin shugaban Bashar A-Asad.
Jaridar Al_qubus ta kara da cewa ofishin jakadancin kasar Siriya a Kuwait bata taba rufe kofarta ba duk tare da cewa gwamnatin kasar Kuwai ta rufe nata a birnin Damascus.
A wani labarin kuma majalisar dokokin kasar Jordan ta bukaci gwamnatin kasar ta fara shirin sake bude ofishin jakadancin kasar a kasar Siriya sannan a maida huldan jakadanci da kasar ta Siriya.