Iran Ta Mayar Da Martani Ga Kasashen Turai
Iran ta mayar wa da kasashen turai martani kan kakaba mata da sabbin takunkumi kan zargin da kasar Danemark ta yi na alakanta wani shirin kisa ga wani mutum a cikin kasarta da tace yana da alaka da wasu jami'an leken asirin Iran.
Da yake maida maratani kan kasashen turai din, ministan harkokin wajen kasar ta Iran, Mohammad Javad Zarif, ya ce abin takaici ne matakin da kasashen suka dauka, a daidai lokacin da suke baiwa munafukan Iran wadanda suka kashe Iraniyawa 12,000 da kuma taimakawa cin zarafin da Saddam ya aikata ga kurdawa na Iraki da kuma wasu kungiyoyin 'yan ta'adda mafaka a kasashensu.
A bayyanin da ya wallafa a shafinsa na Twetter, Mista Zarif, ya ce kasashen turan da suka hada Danemark, Hollande da kuma Faransa duk sun baiwa wadanan kungiyoyin mafaka a kasashensu.
Duk da ikirarinsu na cewa suna goyan bayan yarjejeniyar nukiliyar da kasashen duniya suka cimma da Iran, a ranar Laraba ne kasashen na Turai suka sanar da kakaba wa Iran da takunkumi wanda shi ne tun bayan cimma yarjejeniyar.
Iran ta ce takunkuman sun dogara ne kan zargi marar tsushe da kasar Danemark ta gabatar a farkon watan Oktoba da ya gabata.
Shi ma da yake maida martani kan batun, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, Bahram Qassemi, ya soki matakin wanda ya danganta da abin mamaki, wanda ya ce ya nuna makirci na kasashen Turan a yakin da suka ci sunayi da ta'addanci.
Mista Qassemi, ya kuma bayyana cewa Jamhuriya Musulinci ta Iran, zata dauki matakai na maida martani daidai-ruwa daidai-tsaki kan matakin na kungiyar kasashen turan.