Zarif Ya Gana Da Shugaban Kasar Iraki
(last modified Tue, 15 Jan 2019 13:14:07 GMT )
Jan 15, 2019 13:14 UTC
  • Zarif Ya Gana Da Shugaban Kasar Iraki

Ministan harkokin wajen kasar Iran Dr. Muhammad Jawad Zarif tare da wata babbar tawaga suna gudanar da wata ziyarar aikia kasar Iraki, inda a yau ya gana da shugaban kasar barham Saleh.

A yayin wannan ziyar Zarif ya gana da manyan jami’an gwamnatin kasar, da suka hada da firayi ministan kasar Adel Abdulmahdi, da kuma shugaban majalisar dokokin kasar ta Iraki Muhammad Halbusi da wasu manyan jami’an kasar, a yau kuma ya gana shugaban kasar Iraki Barham saleh.

Tawagar da ke tare da Zarif dai ta hada da manyan daraktoci na ma’aikatun kasuwanci da hrkokin tattalin arziki da makamashi na kasar Iran, dakuma wasu manyan daraktoci na kamfanonin kasar.

An rattaba hannu kan yarjeniyoyo na kara bunkasa harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Iran da Iraki a yayin wannan ziyara.

Ziyarar ta Zarif a Iraki ta zo ne bayan wata irinta da ya kai a kasar India kasa da mako guda da ya gabata, indaa can ma ya gana da manyan jami’an gwamnatin kasar ta India da suka hada da firayi ministan kasar ta India Narendra Modi, da kuma wasu manyan jami’an kasar, inda a can aka cimma wasu muhimman yarjeneiyoyi, da suka hada da na makamshi da sauran bangaroriin cinikyya tsakanin Iran da India.