Jan 26, 2019 11:57 UTC
  • Iran : 'Yan Sanda 2  Sun Yi Shahada A Bardar Imam Khomaini(q)

Mataimakin babban komandan jami'an 'yansanda na JMI a lardin Khuzistan na kudu maso yammacin kasar Iran ya bada sanarwan shahadar yan sanda biyu a safiyar yau Asbar sanadiyar harbi da bindiga wanda wasu mutanen da ba'a tantance ba har yanzun suka yi masu.

Ali Qasimpoor ya bayyana cewa lamarin ya auku ne a garin Bandar Imam Khomaini (q) a dai -dai lokacinda jami'an yansanda a yankin suke sintirin da suka saba a yankin, inda ba zata wani daga cikin wata mota ya bude masu wuta ya kuma yi sanadiyar shahadar yansanda biyu da suke cikin motarsu na sintiri. 

Qasimpoor ya ce a halin yanzu sun fara bincike don gano wadanda suke da hannu wajen wannan aika-aikan, kuma za'a ji karin bayani daga wajensa nan ba da dadewa ba. 

Tags