Iran : Rundinar IRGC Ta Ja Kunnen Kasashen Turai
(last modified Mon, 04 Feb 2019 05:16:56 GMT )
Feb 04, 2019 05:16 UTC
  • Iran : Rundinar IRGC Ta Ja Kunnen Kasashen Turai

Mukadashin kwamandan rundinar kare juyin juya halin Musulinci na Iran, (IRGC), Birgediya Janar Salami, ya ja kunnen kasashen turai akan duk wani yunkurinsu na raba Iran da makamanta masu linzami na kare kanta.

A cewar Janar Salami, karfafa makamai masu linzami na Iran, wani shiri ne na kariya da babu wani mahaluki da ya isa ya dakatar dashi, ko ma wanene kuma koma wacce irin alaka yake da ita da Iran.

Ya kara da cewa kasashen turai wadanda kwanan nan suka gabatar da wani kwarya kwarya shirinsu na cinikaya don kaucewa takukuman Amurka, don tafitar da harkokin kasuwancinsu da kare kaddarorinsu a bangaren man fetur da iskar gaz da kamfanoninsu, kasancewar sun kasa yin gaba da gaba da Amurka, to su kwana da shirin cewa Iran ba zata taba tattaunawa ba kan makamman kare kanta.

Janar Salami, ya kuma kara da cewa, idan kasashen turan sun ci gaba da nacewa kan batun makamman na Iran, da kuma yi mata makarkashiya, to kuwa Iran zata ciba da zurfafa kera makamanta masu linzami.

Ko a ranar Asabar din nan data gabata kasar ta Iran ta sanar da harba wani makami mai linzami kirar '' 'Hoveyzeh'' mai cin zango na kilomita sama da 1,300 a daidai lokacin da kasar ta fara bukukuwan ta na zagayowar ranakun cika shekaru arba'in cif da nasara yuyin juya halin musulinci.